'Yan kabilar Abidat da ke yankin Sirenayka na gabashin Libiya sun mayar da martani ga magoya bayan dan tawaye Haftar Khalifa da ke karya yarjejeniyar tsagaita wuta a yankunansu.
Kabilar Abidat mafi yawan jama'a a gabashin Libiya, wadda kuma Shugaban Majalisar Dokoki ta Tobruk Akilu Salih ya fito daga ciki, ta fitar da wata sanarwa ta faifan bidiyo.
A bidiyon da aka yada a shafukan sada zumunta, shugabannin kabilar sun nuna adawa da yin garkuwa da mutane, kashe su da kaiwa gidaje hare-hare a yankin.
Sanarwar ta bukaci jami'an tsaro da bangaren shari'a su dauki matakin magance wannan matsala, kuma su fara bincike kan kisan gilla da ake yi ga 'yan siyasa da masu fafutuka.
Haka zalika sanarwar ta bukaci a saki dukkan 'yan kabilar Abidat da aka kama tare da daurewa, sannan a dawo da dukiyoyin jama'a da aka sace a Derne da Benghazi, haka kuma a tabbatar wadanda aka raba da matsugunansu sun koma gidajensu.
A ranar 15 ga Maris kabilun yankin Sirenayka suka yi kira da a kori mayakan Haftar daga Benghazi.
A ranar 18 ga watan Maris an gano jikkunan mutane 11 a yankin Bengazi da ke karkashin ikon dan tawaye Haftar Khalifa.