Rikici na ƙazanta tsakanin dakarun soji da mayaƙan M23 a Lubero

Rikici na ƙazanta tsakanin dakarun soji da mayaƙan M23 a Lubero

Rikicin ya tashi ne a garin Lubero da ke da nisan kilomita 150 daga birnin Goma, inda sojojin ƙasar ke amfani da jiragen sama wajen kai hare-hare.

Wannan ne karo na farko cikin kusan shekara guda, da sojojin Congo suka yi amfani da jiragen sama masu saukar ungulu wajen kai wa ƴan tawayen hari.

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewar sojojin gwamnatin Congo sun kasa kwato garin Alimbongo da ke hannun ƴan tawayen, duk da cewa kwanaki biyu da suka gabata sun samu nasarar kwato garuruwan Mambasa da kuma Kanyabi.

Ƙamarin da rikicin ya sake yi a ƴan kwanakin nan dai ya sake ƙara ta’azara ayyukan jinkai a yankin gabashin Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo, inda daruruwan ƴan gudun hijiran da ke Goma suke ta faɗi tashin samun abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)