Kafofin yaɗa labaran Kenya da Uganda sun ruwaito cewa Rebecca mai shekaru 33, wacce ta halarci gasar Olympics da aka kammla a watan daya gabata a birnin Paris, kaso 75 na sassan jikinta ya ƙone bayan harin da saurarinta ya kai mata ta hanyar ƙonata da man fetur a ranar Lahadi da ta gabata, wanda hakan ya sanya adadin mata ƴan wasa da aka kashe a Kenya daga watan Oktoban shekarar 2021, zuwa yanzu ya kai 3.
Ministan wasannin Kenya Kipchumba Murkomen, ya bayyana mutuwar ƴar wasan a matsayin rashin da ya shafi yankin gabashin Afrika baki ɗaya.
A cikin sanarwar da ya fitar, ya ce dole ne su tashi tsaye wajen magance cin zarafin mata da ake samu a yankin, wanda musamman a ƴan shekarun nan ya kunno kai a tsakanin ƴan wasa mata.
Tuni dai ƙungiyar ƴan wasa ta Uganda ta buƙaci yiwa Rebecca adalci, inda ministan wasannin ƙasar Peter Ogwang ya ce Kenya na nan na gudanar da bincike kan lamarin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI