Rashin tsaro ya jefa mutane miliyan 2.8 cikin matsalar rashin abinci a Najeriya

Rashin tsaro ya jefa mutane miliyan 2.8 cikin matsalar rashin abinci a Najeriya

Sakamakon rikice-rikicen da ke faruwa a arewacin Najeriya, mutane miliyan 2.8 na fuskantar matsalar rashin abinci.

Sanadiyyar karuwar matsalar rashin abinci a kasar, an gudanar da wani shiri mai taken Manufofin Manoma na Kasa a babban birnin tarayya Abuja.

A jawabinta, Mary Afan, shugabar kungiyar mata manoma ta Najeriya, ta ce hare-haren kungiyar ta'adda ta Boko Haram da rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma ya shafi ayyukan noma a fadin kasar.

An jaddada cewa mutane miliyan 2.8 har yanzu suna fuskantar matsalar karancin abinci na dindindin a yankin arewacin kasar, Afan ta jaddada cewa matsalar rashin abinci mai gina jiki na ci gaba da yin barazana ga yara a duk fadin kasar.

Afan ta kuma yi gargadin cewa lamarin na ci gaba da ta'azzara ta kuma bukaci gwamnati da ta hanzarta daukar mataki a kai.

Arewacin Najeriya ana yawan samun rikice-rikice lokaci-lokaci saboda rikice-rikicen filaye tsakanin Fulani, wadanda ke aikin kiwon dabbobi, da wasu kabilun da ke harkar noma.


News Source:   ()