Taron da za a yi a Sochi dake kudancin ƙasar, yazo ne bayan da kungiyar tattalin arziƙi ta BRICS ta gudanar da nata a watan jiya, a birnin Kazan na kudu maso yammacin ƙasar.
Rasha dai ta kasance cikin kasashen da ke taka rawar gani a Afrika tun lokacin da take tarayyar Soviet, kuma ta cigaba da inganta tasirinta a nahiyar cikin ƴan shekarun nan.
Kasashe 3 na yammacin Afirka da suka haɗar da Nijar, Mali da Burkina Faso sun juyawa Faransa baya tun bayan juyin mulkin da suka yiwa shugabannin fararen hula tun daga shekarar 2020, kuma suka koma alakar kut da kut da kasar Rashar.
Kasashen Afirka da dama sun bijirewa matsin lamba na shiga cikin takunkuman da ƙasashen yamma suka ƙaƙabawa Rasha kan yaƙin da take gwabzawa a Ukraine tun daga shekarar 2022.
Rasha ta sayarwa wasu kasashen Afirka da makaman da kudin su ya zarce dala biliyan 5 a shekarar da ta gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI