Ƙungiyar Al-Qaeeda ce dai ta yi garkuwa da ma’aikatan kamfanin Rahsa da ke bincike kan ma’adanan ƙarƙashin ƙasa tun watan da ya gabata.
A wani faifan bidiyo da ƙungiyar JNIM ta fitar ya nuna ma’aikatan guda biyu da aka yi garkuwa da su a yankin Tillaberi mai fama da rikici.
A cikin bayanan da mayaƙan suka yi basu bayar da cikakken jawabi kan lokaci da kuma gurin da suka naɗi bidiyon ba, kana kuma basu buƙaci kuɗin fansa ba.
Ta cikin wata takarda da mahukuntan Rasha suka fitar, sun ce mutanen biyu da aka yi garkuwa da su sun haɗar da Oleg Gret ɗan asalin Rasha sai kuma Yuri Yurov ɗan asalin Ukraine.
Ƙididdiga ta kuna cewa yayin harin mayaƙan na JNIM sun yi garkuwa da mutane 4 tare da ƙashe sojojin Nijar da ba’a bayyana adadinsu ba a harin da ta kai ranar 18 ga watan yulin da ya gabata.
Tuni dai Rahsa ta sanar da aikewa da jami’ai zuwa ƙasashen Nijar da kuma Mali don neman taimakon su da kuma bayani kan yadda za’a kuɓutar da mutanen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI