Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Rasha Maria Zakharova ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na RIA Novosti cewa, sakamakon rashin nasara kan Rasha, yanzu gwamnatin Volodymyr Zelensky ta buɗe sabon daga na biyu a Afirka.
Zakharova ta zargi Ukraine ta taimaka wa ƙungiyoyin ta'addanci a ƙasashen nahiyar Afirka da ke abokantaka da Moscow.
Harin da ya tada hankaliƳan awaren Abzinawa a Mali sun ce sun kashe kimanin sojin hayar Waganer ta Rasha 84 da kuma sojojin Mali 47 a wani hari da suka kai arewacin Mali a watan jiya.
Mali ta zargi wani babban jami'in Ukraine wanda ya amince da rawar da ƙasarsa ta taka a harin, wanda ya sa ta yanke huldar jakadanci da Ukraine a ranar 5 ga watan Agusta.
Kakakin gwamnatin ƙasar Kanar Abdoulaye Maiga ya ce gwamnatin Mali ta kadu matuka da samun labarin Andriy Yusov, kakakin hukumar leken asirin sojin Ukraine, GUR.
Ita ma Nijar ta sanar da matakin katse duk wani huldar diflomasiya da Ukraine.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI