Rasha ce ke taimakon ɓangarorin da ke yaƙi a Sudan don cikar muradanta- Amurka

Rasha ce ke taimakon ɓangarorin da ke yaƙi a Sudan don cikar muradanta- Amurka

Linda Thomas ta bayyana zargin mai girma ne yayin da take tsokaci akan matakin da Rasha ta ɗauka a watan Nuwamba, na hawa kujerar naƙi kan ƙudurin da Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya na bayar da umarnin tsagaita wutar nan take a Sudan, duk da cewar ragowar kasashe 14 masu kujerar dindindin sun goyi bayan hakan.

A lokacin da aka nemi ƙarin bayani kan zargin Jakadiyar Amurka, sai kakinta ya kada baki ya ce suna sane da yadda Rasha ke cigaba da hada-hadar cinikayyar Zinare tsakaninta da gwamnatin sojin Sudan, wanda ke tatater da manufa ta kare muradunta, dan haka suke yi A -Wadai da duk wani taimako walau na kudi ko makamai da Rashan ke baiwa sojojin kasar da kuma ‘yan tawayen dake rikici dasu.

Sai dai mataimakin Jakadan Rasha a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya Dmitry Polyanskiy ya bayyana iƙirarin na Amurka a matsayin abin kunya, la’akari da yadda take yin gaban kanta wajen tuhumar sauran ƙasashe ba tare da hujja ba.

A watan Afrilun shekarar 2023, yayin da ake shirin maido da mullkin farar hula, ƙazamin yaƙi ya ɓarke tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF da a yanzu ke tawaye, lamarin da ya haifar da tagayyarar fararen hula mafi muni a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)