Ranar Ruwa ta Duniya: Har yanzu ba ta sauya zani ba a Najeriya

Ranar Ruwa ta Duniya: Har yanzu ba ta sauya zani ba a Najeriya

An bayyana cewar, yara kanana miliyan 26,5 ne ba sa samun tsaftataccen ruwan sha a Najeriya.

Babban Jami'in Asusun Tallafawa Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya Peter Hawkins ya fitar da sanarwa albarkacin zagayowar Ranar Ruwa ta Duniya ya inda ya ce, jama'ar yankin suna amfani da ruwan kudiddifai da na gulabe da ya taru bayan saukar ruwan sama na mintuna zuwa 30.

Hawkins ya shaida cewa, yara kanana miliyan 26,5 ne ba sa samun tsaftataccen ruwan sha a Najeriya.

Jami'in ya fadi cewar, wannan yanayi ne mara kyau matuka, a duniya ana fuskantar matsalar samun tsaftataccen ruwan sha, kuma yara kanana ne suka fi illatuwa da wannan matsala. Idan aka gina rijiyoyi, yara na kin zuwa makaranta saboda suna tafiya debo ruwa.

Hawkins ya ci gaba da cewa, har yanzu a Najeriya ana fuskantar rashin daidaito wajen samun tsaftataccen ruwan sha a tsakanin 'yan kasar, kaso 86 na 'yan Najeriya ba sa samun ruwan sha mai tsafta.

Ya kuma ce, UNICEF na aiki tare da mahukuntan Najeriya don samar da ruwan sha tsafta, kuma akwai bukatar gudanar da aiyuka da dama don magance wannan matsala.


News Source:   ()