A watan Fabrairun da muke ciki ne shugaba Donald Trump ya sanar da katse tallafin da Amurka ke bai wa ƙasar, bayan da ya bayyana rashin gamsuwa kan wata doka da Ramaphosa ya rattaba wa hannu da ta kunshi karɓe wasu filaye daga hannun jama'a idan buƙatar hakan ta taso ba tare da biyan komai ba, baya ga ƙarar da Afrika ta Kudu ta shigar da ƙasar Israila mai ƙawance da Amurka a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.
Ramaphosa ya sanar yayin wani taro a Johannesburg cewa yana so ƙurar ta lafa bayan dokar da Trump ya ayyana na katse ba su tallafi, kodayake ya bayyana shirinsa na zuwa Washington DC domin gyara alaƙar.
Duk da cewa Ramaphosa bai faɗi irin yarjejeniyoyin da yake fatan za su ƙulla da Amurkan ba, amma ana kyautata zaton za su shafi harkokin kasuwanci, alaƙar ƙasa da ƙasa da kuma siyasa.
Ƙasar Afrika ta Kudu dai bata dogara ɗari bisa ɗari kan tallafin Amurkan ba, to sai dai ana fargabar hakan zai shafi yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Amurka da wasu ƙasashen Afrika, wanda ke ba su damar shigar da kayayyaki cikin ƙasar ba tare da kuɗin fito ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI