Wannan ziyarar ta Firaministan Sifaniya Pedro Sanchez za ta mayar da hankali kan ƙarfafa alaƙa da ƙasashen Mauritania Senegal da Gambia kasancewarsu hanyoyin da jiragen ruwan da ƴan gudun hijirar ke bi cikin yanayi mai haɗari.
Wasu alkaluman hukumar kula da ƴan gudun hijira ta tarayyar Turai ta ce alƙaluman masu tsallaka iyaka sun ƙaru zuwa kaso 154, abinda ya ƙara adadin mutane 21,620 masu tsallakawa zuwa tsibirin Canary a watanni 7 na farkon wannan shekara.
Karuwar ƴan gudun hijirar ya haddasa babban ƙalubale dangane da kayan agaji a tsiburan dake sifaniyar, abinda ya sa hukumomi suka ce a yanzu suna ajiye yan gudun hijira a tantunan sojoji.
Hukumomin sifaniya sun ce akwai fargabar sama da ƴan gudun hijira dubu 150 ne zasu tsallaka iyaka cikin yanayi mai cike da haɗari a watanni ma su zuwa.
Ƴan sandan Sifaniya sun jima suna aiki a Afirka ta yamma domin tabbatar da tsaron iyaka ta hanyar sanya maƙudan kuɗi da tallafin tsaro dangane da batun kwararar yan gudun hijirar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI