Biya mai shekaru 92 da ya shafe shekaru fiye da shekaru 42 a karagar mulkin Kamaru, ya bayyana cewa hatta bayan shekarar ta 2025 ya na hango kanshi a matsayin shugaban Kamaru, kalaman da kai tsaye ke nuna sha’awarsa ta sake tsayawa takara don ci gaba da jan ragamar ƙasar.
Shekarar da muka shiga ta 2025 ita ce bisa doka yakamata Kamaru ta kira zaɓen shugaban ƙasa wanda masana ke bayyana yiwuwar ya iya zama babban ƙalubale matuƙar shugaban ya sake nuna sha’awar tsayawa takarar zabe.
A baya-bayan nan ana ganin yawaitar masu neman tsayawa takara hatta daga cikin jam'iyyar shugaban na Kamaru, lamarin da baya rasa nasaba da tsawon lokacin da ya ɗauka a kujerar mulkin ƙasar.
Ko a shekarar da ta gabata ta 2024 anga yadda jita-jitar mutuwar shugaban ta yamutsa hazo ba kaɗai a ƙasar ta Kamaru ba har ma da sauran sassan Afrika, lura da kasancewarsa shugaba na biyu mafi daɗewa a madafun iko a nahiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI