Ma'aikatar harkokin wajen Ivory Coast ta ce ta mayar da jakadanta a Lebanon da ma'aikatan diflomasiyyarta da ke Beirut a ranar Asabar din nan zuwa gida.
Alassane Ouattara Shugaban kasar Cote D'Ivoire © Issouf Sanogo / RFIRahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Alassane Ouattara ne "ya yanke shawarar mayar da 'yan kasarsa da kuma jami'an diflomasiyyar da ke zaune a Lebanon".
Bisa la'akari da "karin tashin hankali tsakanin sojojin Isra'ila da mayakan Hezbollah", kasar Ivory Coast ta kaddamar da "aikin mayar da 'yan kasar Cote D’Ivoire" wanda ya shafi 'yan kasar kusan ɗari da ke zaune a Lebanon,wanda da farko 60 ne daga cikinsu sun nuna sha'awar komawa kasar.
Wasu daga cikin hare-haren Isra'ila a Beirut © AP - Hussein MallaKimanin 'yan Ivory Coast 20 ne aka riga aka maido da su zuwa kasar a ranar Juma'a, ba tare da wata sanarwa a hukumance ba.
'Yan Ivory Coast da suka dawo dan kashin kan su na cikin jiragen kamfanoni masu zaman kan su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI