Orano ya kai gwamnatin Nijar kotu kan batun mahakar Imouraren

Orano ya kai gwamnatin Nijar kotu kan batun mahakar Imouraren

Orano, ya ce ya dau matakin ne saboda duk wani yunkuri da aka yi na sansantasu tun daga lokacin da aka kwace masa lasisin na Imouraren rana 19 ga Yulin 2024 ya cutura.

Bayanai sun yin nuni da cewa a halin yanzu kamfanin Orano ya damka batun takaddamar ga wasu kwararrun  lauyoyi da ke zaune a birnin Paris domin a bi  masa da hakokinsa.

A farkon watan Disamba da muke ciki Orano ya fitar da sanarwa  cewa gwamnatin mulkin sojin Nijar ya karbe iko da ayyukan sarrafa ma’adinin Uranuim  a cibiyar  Somair dake yankin  Agadas da ya ke da hanun jarin kaso 63% a ciki.

A ‘yan watannin nan kasa Nijar ta bayyana karara shirinta na kawo sauye sauye a fanin ma’adinan karkashin kasa da take dasu  yayin da ta karkata alakarta zuwa kasashen Rasha, Iran da Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)