Nijar ta kulla yarjejeniya da Rasha kan samar da tauraron dan adam guda uku domin inganta tsaro a yankin Sahel

Nijar ta kulla yarjejeniya da Rasha kan samar da tauraron dan adam guda uku domin inganta tsaro a yankin Sahel

 

Kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da ke karkashin mulkin soji tun bayan juyin mulkin da aka yi tun shekara ta 2020, sun hade ne a watan Satumban 2023 a karkashin kungiyar kawancen kasashen Sahel (AES), bayan da suka yanke alaka da Faransa wace ta fito ta kuma nuna  kiyayya ga Rasha.

Makwabtan duk suna fama da tashe-tashen hankulan masu da'awar jihadi da ya barke a arewacin Mali a shekarar 2012 ya kuma bazu zuwa Nijar da Burkina Faso a shekarar 2015.

Birnin Yamai Birnin Yamai © Omar Hama / AP

Yarjejeniyar ta shafi tauraron dan adam na sadarwa, wani na hangen nesa da kuma na uku na kariya, in ji ministan sadarwa na Jamhuriyar Nijar Sidi Mohamed Raliou a wajen bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar a Yamai babban birnin kasar.

Wannan aiki zai dau shekaru hudu tsakanin kasar ta Nijar da Rasha.

Shugabanin kasashen Nijar,Mali da Burkina Faso Shugabanin kasashen Nijar,Mali da Burkina Faso REUTERS - Mahamadou Hamidou

Gidan rediyon gwamnatin Nijar ya ruwaito cewa a halin da ake ciki Glavkosmos ya amince ya ba da rancen kayan aiki cikin lokaci ,ministan ya ce "wannan muhimmin aikin yana cikin tsarin mulkin kasashenmu."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)