Nau'ikan giwaye na Gab da ƙarewa a Afrika

Nau'ikan giwaye na Gab da ƙarewa a Afrika

Masu bincike sun gabatar da wani rahoto da su ka bayyana a matsayin cikakken nazari kan halin da nau’ikan giwaye biyu na Afrika ke ciki , inda su ka yi amfani da alƙalumma binciken da su ka gudanar a dazuka 475 daga kasashe 37 daga shekarar 1964 zuwa 2016.

Rahoton ya kuma bayyana nau’ikan giwayen da ke neman ɓacewa da su ka haɗa da na daji da kuma na hamada.

Binciken dai ya nuna yawan giwayen hamada ya ragu da aƙalla kaso 70 cikin 100, yayin da yawan giwayen dajin ya ragu da aƙalla kaso 90 cikin 100 daga waɗannan dazukan da aka bincika.

Duka-duka dai jimillar giwayen da su ka ragu na waɗannan nau’uka biyun ya kai kaso 77 cikin 100.

Bayanai na nuna cewa a yayin da ake samun raguwar giwaye a wasu yankuna, adadinsu na karuwa ne a wasu wurare da ake kai su ajiya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)