Namibia za ta yanka giwaye don raba naman ga ƴan ƙasar da ke fama da yunwa

Namibia za ta yanka giwaye don raba naman ga ƴan ƙasar da ke fama da yunwa

Kazalika gwamnatin za ta yanka dorinar ruwa 30 da ɓauna 60 da barewa 50 da kuma ragunan daji 100 da jakunan dawa 300 da bunsurun daji 100.

Tuni gwamnatin ta sa kwararrun mafarauta suka farauto namun dajin daban-daban har guda 157 da nauyin namansu ya zarta kilogiram dubu 58.

Za a yi watandar namun dajin ne a wasu wurare da gwamnatin ta keɓe da suka haɗa da gandun dajin da ake kula da dimbin dabbobin da adadinsu ya wuce ƙima kamar yadda Ma'aikatar Muhalli ta Ƙasar ta sanar a ranar Litinin.

Ƙasashen yankunan Afrika ta Kudu na fama da matsanancin fari mafi muni cikin gomman shekaru, lamarin da ya tilasta wa Namibia cinye kashi 84% na abincin da ke rumbun gwamnati kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya.

Bayanai na nuna cewa, kusan rabin mutanen Namibia za su tsunduma cikin musibar ƙarancin abinci nan da wasu ƴan watanni masu zuwa.

Ma'aikatar Kula da Muhalli ta Ƙasar ta ce akwai buƙatar gwamnati ta tinkari wannan al'amari domin hana mutane shiga mawuyacin hali na tagayyara a dalilin ibtila'in na fari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)