Namibia ta bi sahun Afirka ta Kudu da kungiyoyin masu zaman kansu da dama a nahiyar wajen yin watsi da matakin da Hukumar Tarayyar Afirka ta yanke na baya -bayan nan na bai wa Isra’ila matsayin mai sa ido a tarayyar.
Penda Naanda, babbar daraktar ma'aikatar huldar kasa da kasa ta Namibia, ta ce "Bada matsayin mai sa ido ga mai mamaye ya sabawa ka'idoji da manufofin Dokar Tsarin Mulki na Tarayyar Afirka."
Shugaban Hukumar Tarayyar Moussa Faki Mahamat a ranar 22 ga watan Yuli ya karbi takardun aiki daga Aleli Admasu, Jakadan Isra’ila a Habasha, Burundi da Chadi.
Wannan ya ba da matsayin mai sa ido ga kasar yahudawa a tarayyar nahiyar, wanda mafi yawan membobinta ke adawa da haramtacciyar kasar Isra'ila akan mamaye Falasdinu.