Kawo yanzu a fadin duniya annobar Korona ta yi ajalin mutum miliyan 2 da dubu 429 da 825, inda kuma mutum miliyan 110 da dubu 35 suka kamu da cutar a yayinda mutum miliyan 84 da dubu 865 suka warke daga cutar a doron kasa.
A cikin awanni 24 da suka gabata a kasar Indiya an samu karin rasuwar mutum 109 inda kuma mutum dubu 11 da 795 suka harbu da cutar. Kawo yanzu a kasar mutum miliyan 10 da dubu 937 da 320 sun kamu da cutar a kasar.
A kasar Najeriya in cutar ta yi ajalin mutum dubu 1 da 777 da kuma kama mutum dubu 148 da 296 an sayi allurar riga-kafin Korona na doz miliyan 1.4 daga kanfanin AstraZenec wanda za a bayar da dubu 500 na farko a watan Febrairu.