![Najeriya ta samu naira biliyan 181 daga lantarkin da ta sayarwa ƙasashen waje](https://iqra-media.s3.eu-west-2.amazonaws.com/public/AP060314019401__ScaleWidthWzEwMDBd.jpg)
Hukumar Kididdigar Najeriya NBS ce ta fitar da al’kaluman, inda ta ce tsakanin watan Janairu zuwa Satumbar wannan shekara ta 2024 ne Najeriyar ta samu ƙudin da ya haura Naira biliyan 181.62 daga wutar lantarkin da ta tura zuwa ƙasashen Togo da Benin da kuma Jamhuriyar Nijar.
Takaddar bayanai ta nuna cewa an fitar da wutar lantarkin da darajarsu ta kai Naira biliyan 58.65 zuwa kasashen uku a cikin rubu'in farko na shekarar. Hakan ya biyo bayan Naira biliyan 63.28 a kwata na biyu da kuma Naira biliyan 59.69 a watanni uku na ƙarshen shekarar.
Hukumar kiɗiddigar Najeriyar ta ce kamfanonin rarrabawa wutan lantarki sun samu ƙudin shiga da ya kai Naira biliyan 391.71 daga abokan huldar na cikin gida Najeriya kimanin miliyan 12.99 a cikin rubu’i na 2 na shekarar 2024.
Daga cikin waɗannan kwastomomi, miliyan 5.92 na amfani da mita, yayin da miliyan 7.07 na biyan wuta ne ta kiyasi.
Kamfanin samar da lantarki ta Ikeja dake Legas (IEDC) ita ce kan gaba a yawan samun ƙudin shiga, inda ta samu Naira biliyan 80.17, sai Eko (EKEDC) a Legas da Naira biliyan 68.03 sai Abuja (AEDC) da Naira biliyan N63.97.
Ibadan (IBEDC) ta haɗa Naira biliyan 39.58.
Benin (BEDC) ta samu Naira biliyan 30.84.
Fatakwal (PEDC) ta samu Naira biliyan N29.50.
Enugu (EEDC) nada Naira biliyan 27.11.
Kano (KEDC) ta tattara Naira biliyan 19.28.
Jos (JEDC): Naira biliyan 15.54.
Kamfanin samar da lantarkin Kaduna (KDEDC) ya tara Naira biliyan 13.23.
Sai kuma Yola (YEDC) da Naira biliyan 4.49.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI