Najeriya ta sayi jiragen yaki 6 samfarin "A-29 Super Tucano" daga Amurka a matsayin wani bangare na yaki da ta'addanci.
A cikin wata rubutacciyar sanarwa, Kakakin Rundunar Sojan Sama ta Najeriya (NAF) Edward Gabkwet ya bayyana cewa jiragen sama 6 na 12 "A-29 Super Tucano" da aka saya daga Amurka a wani bangare na kokarin yaki da ta'addanci sun isa Najeriya.
Gabkwet ya lura da cewa jiragen da suka isa jihar Kano an mika su ne ga Ministan Tsaron Nijeriya, Bashir Salihi Magashi, da Kwamandan Sojojin Kasa, Manjo Janar Farouk Yahaya da kuma Kwamandan Sojojin Sama Laftanar Janar Isiaka Oladayo Amao.
Gabkwet ya ba da bayanin cewa sauran jirage 6 za su iso kasar a cikin Oktoba.
Sayen jiragen da aka shirya amfani da su kan kungiyar ta'addancin ta Boko Haram, shugaban kasar Amurka na baya Barack Obama ne ya jinkirta sayar da jiragen, bisa hujjar take hakkin bil'adama da sojojin Najeriya suka yi.
Jiragen da da farko aka bayyana za'a kawo kasar Najeriya a watan Maris din 2020 an jinkirta zuwa 2021.
An ruwaito cewa Najeriya ta biya dala miliyan 400 don jiragen, kuma a yarjejeniyar an shirya samar da kayan aikin soja da horo ga sojojin Najeriya.
Ana amfani da jiragen yaki na "A-29 Super Tucano" a Afirka a kasashen Ghana, Angola, Burkina Faso da Mauritania.