Najeriya ta ce bata ji daɗin yunƙurin ficewar ƙasashen AES daga ECOWAS

Najeriya ta ce bata ji daɗin yunƙurin ficewar ƙasashen AES daga ECOWAS

Mai taimakawa shugaban Najeriya Bola Tinubu kan yaɗa labarai Abdul-aziz Abdul-aziz ne ya bayyana matsayar ƙasar a tattaunawarsa da RFI Hausa.

Abdul-azizi ya ce akwai buƙatar Nijar ta kara nazari mai zurfi kafin kammala ficewa daga wannan kungiya ta ECOWAS, duba da cewa an sake ɗebar musu lokaci har wata 6 domin yin tunanin sake komawa ƙungiyar..

A cewarsa al’ummomin wannan yanki al’umma ɗaya ce domin akwai daɗaɗɗiyar alaƙa ta auratayya da zamantakewa da ke tsakanin al’ummar yankin.

Mai taimakawa shugaban Najeriya Bola Tinubu kan yaɗa labarai Abdul-aziz Abdul-aziz ya ƙara da cewa idan ƙasashen suka aiwatar da ficewa daga ECOWAS to al’ummar ƙasashen ne za su sha wahala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)