Ķasar Najeriya ta bayyana cewa kimanin mutane miliyan 230 na fuskantar matsalar rashin abinci a yankin Saharar Afrika.
Ministan tattalin arzikin Najeriya, Zainab Ahmed da take jawabi a taron "Samar da Abinci a Afirka" da Asusun Lamuni ta (IMF) ta shirya ta yanar gizo ta bayyana cewa matsalar rashin abinci ya kai halin kakanikayi a Afirka inda ta bayyana cewa hadi da Najeriya akwai mutum miliyan 230 dake fama da matsalar rashin abinci a yankin Sub Saharan Afrika.
Ministan ta kara da cewa harkokin noma ya fuskanci matsala da dama a Najeriya, inda ta kara da cewa lokaci ya yi da za a kara bunkasa harkokin noma a Nahiyar Afirka.
Ta kuma yi kira ga hadin gwiwa a matakin kasa da kasa domin magance matsalar rashin abinci a doron kasa. Inda ta jaddada cewa samar da wadataccen abinci nada matukar muhimmanci ga alumma da kuma ga lamarin bunkasa tattalin arzikin kasa.