Najeriya da Nijar da kuma Aljeriya sun cimma yarjejeniyar shimfiɗa bututun gas zuwa Turai

Najeriya da Nijar da kuma Aljeriya sun cimma yarjejeniyar shimfiɗa bututun gas zuwa Turai

Bututun, wanda ake kira (TSGP), zai tashi ne daga Najeriya ya ratsa Jamhuriyar Nijar zuwa Aljeriya, kafin ya tsallaka teku Meditaranean zuwa Turai.

A yarjejeniyar, ƙasashen 3 sun amince su yi amfani da bututun Transmed wanda Aljeriya ke amfani da shi don bai wa Italiya makamashin gas, sai a yanzu maimakon Italiya kawai da ke cin gajiyarsa, za a riƙa tura makamashin zuwa sauran ƙasashen Turai.

Yarjejeniyar da wakilan ƙasashen uku suka rattaba wa hannu ranar Talata da ta gabata, ta fayyace adadin kuɗaɗe da tsawon lokacin da ake buƙata don aiwatar da wannan aikin, sai kuma batun biyan diyya da kuma zaɓen ƙmfanonin da za su aiwatar da wannan aiki.

Tun a shekara ta 2009 ne ƙasashen 3 suka tattaunawa domin shimfiɗa wannan bututu mai tsawo kilomita dubu 4 da 128, kuma tun a wancan lokaci an kiyasta cewa ana bukatar Dala bilyan 10 domin aiwatar da aikin.

Rikicin Rasha da Ukraine ne ya ƙara zaburar da waɗannan ƙasashe domin gaggauta aiwatar da wannan aiki na bututun iskar gas, musamman lura da cewa tun a 2022 mafi yawan ƙasashen Turai sun bayyana aniyarsu ta daina dogara da Rasha domin samun makamashin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)