A nahiyar Afirka baki daya, Najeriya ce kasar da aka samu mafi yawan batan mutane inda mutane dubu 24 suka bata.
Kakakin Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Cross a Najeriya Aliyu Dawobe, albarkacin zagayowar ranar wadanda suka bata ta duniya ya fitar da sanarwa inda ya ce, mutane dubu 44 sun bata a Afirka.
Dawobe ya bayyana cewa, dubu 24 daga cikin wannan adadi sun bata a Najeriya, kasar ce ke da mafi yawan wadanda suka bata a Afirka.
Dawobe ya kara da cewa, sama da kaso 90 na batan mutane ya afku ne a yankin arewa maso-gabashin Najeriya da ake fama da hare-haren 'yan ta'adda, kuma kaso 57 na wadanda suka batan yara ne kanana.
Dawobe ya ci gaba da cewa, sakamakon rigingimu a Afirka, tun daga 2020 zuwa yau sun samu karuwar adadin mutanen da suka bata.
Ya ce, duk da wahalar da ake fuskanta saboda annobar Corona, amma sun yin iya kokarinsu doon nemo wadanda suka bata a kasar.