Abin mamakin shine, yadda Najeriya ta gaza shiga cikin kasashe goman farko na nahiyar da ke fama da wannan bashi, duk kuwa da dimbin bashin da take karbowa
Akwai kasashen goma da suka sha gaban sauran takwarorinsu na nahiyar wajen karbar bashin, wanda masana ke ganin suna amfani da basukan da suka ciyo din ne domin cike gibi, musamman a kasafin kudadensu, daidai lokacin da suke fama da mashassharar tattalin arziki.
Duk da cewa IMF na basu basussukan a duk lokacin da suka mika bukatar hakan, sai dai akwai sharudda masu tsauri da ake gindaya musu, kamar janye tallafi, karya darajar kudadensu da kuma tsuke bakin aljihu.
Wadannan sune kasashe da suka kasance na goman farko wajen ciyo bashi daga IMF.
Masar: it ace kan gaba da bashin dala biliyan 9.45, yayin da kasar ke cikin tsaka mai wuya game da matsalolin tattalin arziki, Kenya ce kasa ta biyo da yawan bashin da ya kai dala 3.02, inda Angola ta kasance a matsayi na uku da yawan bashin dala biliyan 2.99, bayan da ta dogara da IMF domin kayyade farashin mai da kuma inganta tattalin arzikin ta.
Ghana ta kasance a matsayi na hudu, inda ta ciyo bashin dala biliyan 2.25, yayin da kasar ke fama da karyewar darajar kudi da kuma matsi na tattalin arziki itama, sai kuma Ivory Coast da ta kasance a matsayi na biyar da bashin da ya tasamma dala biliyan 2.19, wanda ta karba domin aiwatar da tsare-tsaren da suka taimaka wajen bunkasa kasar.
Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ce kasa ta shida da adadin bashi da ya kai dala biliyan 1.6, wanda tace ta karba ne domin magance matsalolin da suka dabaibaye bangaren tattalin arziki, duk da cewa kasar tana da tarin albarkatun kasa.
Sauran kasashen sune Habasha da bashin dala biliyan 1.31, sai Afirka ta Kudu da ake bin bashin dala biliyan 1.14, yayin da Kamaru ta ciyo bashin dala biliyan 1.13, sai kuma kasa ta goma wato Senegal da karbo bashin dala biliyan 1.11 domin daidaita tattalin arzikinta.
Dogaro da kudaden IMF na kara nuna tababa kan hada-hadar kasuwanci da kasashen Afirka ke fuskanta, yayin da suke kai ruwa rana kan yadda za su magance bukatun kasafin kudi nan take da kuma cimma muradun ci gaba mai dorewa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI