Nahiyar Afrika zata zama gidan cibiyar lantarki mafi girma a duniya

Nahiyar Afrika zata zama gidan cibiyar lantarki mafi girma a duniya

Matuƙar aka kammala ginin cibiyar lantarkin zata iya samarwa da kafatanin ƙasashen Afrika wuta ba tare da wata matsala ba.

Madatsar ruwan da tuni aka raɗawa suna Inga Dam zata sami karfin samar da Megawhatts dubu 44 na wutar lantarki, yayin da aikin zai laƙume dala biliyan 80.

Bayanai sun ce tuni Jamhuriyar dimokraɗiyyar Congo ta bayar da filin da za’a yi aikin ginin madatsar ruwan.

Wani bincike ya nuna cewa cibiyoyin kuɗin sun amince da jamhuriyar dimokraɗiyyar Congo don yin wannan aiki da nufin taimakamata wajen habbaka tattalin arzikinta da kuma alkinta manya kogunan da ƙasar ke da su da suke barazanar ƙafewa.

Baya ga wannan makekiyar cibiyar wutar lantarki, za kuma a gina wasu ƙananan guda 6 duk a ƙasar waɗanda zasu kasance ƴan jiran ko ta kwana.

Wani rahoton bincike ya nuna cewa an ɗauki sama da shekaru 10 ana tattaunawa tsakanin ƙasar da cibiyoyin ƙudin kan wannan aiki, sai dai kuma rashin tabbas kan yadda ƙasar zata gudanar da aikin ya hana a fara shi, har sai yanzu da cibiyoyin suka amince suyi aikin da kansu.

Rahotanni sun nuna cewa aikin ya sami chachaka daga ƴan adawa da ke ganin kamata yayi cibiyoyin kudin su mayar da hankali kan zuba jari a fannin ma’adanai kasancewar wannan na cikin arzikin da ƙasar ke taƙama da shi.

To sai dai kuma samar da wutar lantarkin ka iya biyan wannan buƙata ta su, la’akari da yadda za’a tsara shi ta yadda kai tsaye za’a rika amfani da wutar wajen hakar ma’adanan a zamanance.

Tuni ƙasashen Afrika ta Kudu da Najeriya suka mika ƙoƙon barar basu wutar da zarar an kammala aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)