Nahiyar Afirka ta yi asarar dala biliyan 190 saboda Korona

Nahiyar Afirka ta yi asarar dala biliyan 190 saboda Korona

Annobar COVID-19 ta haifar da asarar dala biliyan 190 ga tattalin arzikin Afirka, in ji shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB).

Akinwumi Adesina na magana ne a taron shekara-shekara na AfDB 2021 wanda aka gudanar ta yanar gizo.

Adesina ya ce annobar ta tilastawa mutane miliyan 30 fadawa cikin talauci yayin da ya lura cewa kimanin mutane miliyan 39 na iya talaucewa a ƙarshen 2021.

AfDB ya gudanar da bincike mai kwari akan tattalin arzikin Afirka tare da kaddamar da dala biliyan 3 don taimakawa.

Bankin ya kuma sanar da samar da dala biliyan 10 domin bayar da agajin gaggawa ga lamurran annoba.

Adesina ya kara da cewa,

"Mun samar da dala miliyan 28 ga Cibiyoyin Kula da Rigakafin Cututtuka na Afirka. Mun ceci rayuka da dama."

Ya kuma jaddada cewa, Nahiyar na murmurewa, tare da matsakaicin adadin kudin shigar cikin gida na (GDP) da karuwar kaso 3.4 cikin dari a shekarar 2021.


News Source:   ()