Mutumin da ya yi yunkurin cakawa wanda ya jagoranci juyin mulkin 24 ga Mayu a Mali kuma ya zama Shugaban Kasar Assimi Goita wuka ya mutu a lokacin da ake tsare da shi a hannun jami'an tsaro.
Sanarwar da gwamnatin Mali ta fitar ta bayyana cewa, maharin da ba a bayyana sunansa ba ya suma a inda ake tsare da shi inda ya kuma ce ga garinku nan bayan an kai shi asibiti.
Sanarwar ta ce, bayan an kammala gwaje-gwaje ne za a gano musabbabin mutuwar mutumin.
A ranar Babbar Sallah ne a lokacin da Assimi Goita ya gama Sallar Idi a Masallacin Juma'a na Ulu da ke Bamako wani mutum ya lallabo ta bayansa da wuka da nufin caka masa.
An kama maharin tare da wani mutum daya da ke tare da shi, Goita kuma ya kubuta ba tare da samun ko kwarzane ba.
An fara gudanar da bincike game da lamarin.