Shirin samar da agajin na musamman da majalisar ta kira, tace za a yi amfani da shi wajen tallafawa mutane sama da miliyan 20 daga cikin adadin sama da miliyan 30 da ke bukatar agaji.
Sudan dai ta fada cikin yaki tun watan Afrilun 2023, tsakanin ‘yan tawayen RSF da kuma dakarun gwamnati, abin da hukumomi na duniya suka ce ya haifar da tsananin yunwa
Dubban mutane aka kashe a wannan yaki, inda sama da mutum miliyan takwas suka rasa muhallansu, wanda hakan ya kara adadin miliyoyin ‘yan gudun hijira kan miliyan biyu da dubu dari bakwai da ake da su a baya.
Sama da mutum miliyan uku ne suka tsallaka zuwa kasashe makwabta, inda MDD ta ayyana cewa Sudan ce kan gaba a halin yanzu na yawan ‘yan gudun hijira da kusan rabin al’ummar kasar ke hijira.
Tuni aka ayyana cewa yunwa ta yi kamari a yankuna biyar na kasar, kuma ana fargabar za a sake samun hakan a wasu yankuna biyar daga nan zuwa watan Mayu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI