Mutum miliyan 200 ka iya kamuwa da Corona a Afirka

Mutum miliyan 200 ka iya kamuwa da Corona a Afirka

Hukumar Lafiya ta Duniya watau WHO ta bayyana cewa  a Nahiyar Afirka Corona ka iya kashe mutum dubu 150,000 kuma kusan daya bisa hudun biliyan ka iya kamuwa matukar ba’a dauki matakan da suka dace ba.

Marubucin Mujallar BMJ Global Health, ya yi hasashen cewa za’a iya samun karancin matsalar mutuwa da kamuwa da cutar idan aka kwatanta da Turai da Amurka, amma kuma kasancewar yadda da yawan kasashen Afirka suna rikon sakainar kashi game da matakan da aka bayyana a dauka cibiyoyin lafiyar kasashen ka iya cika su batse.

Hakan dai jan kunne ne ga kasashen dake da rubabbun cibiyoyin lafiya da kuma basa bin dokar kulle.

Masana a Hukumar WHO a sashen Afirka sun bayyana cewa a kasashe 47 cutar ka iya kamari sai dai sun ware kasashen Misira, Djibouti, Libya, Morocco, Somalia, Sudan da Tunisia.

Hasashen ya kara da cewa kusan mutum miliyan 231 kimanin kaso 22 cikin darin yawan al’umman nahiyar ka iya kamuwa da cutar a cikin shekara daya ba tare da ma sun nuna alamun suna dauke da cutar ba.

Haka kuma miliyan 4.6 za’a kwantar dasu a asibiti, inda dubu 140, 000 rashin lafiyarsu zai tsananta  dubu 89,000 kuwa zasu kasance a dakunan kulawar gaggawa, kusan fiye da dubu 150 ka iya rasa rayukansu a nahiyar baki daya.


News Source:   www.trt.net.tr