Mutum akalla 100 sun mutu saka makon hadarin tankar mai a Jihar Neja

Mutum akalla 100 sun mutu saka makon hadarin tankar mai a Jihar Neja

Bayanai sun ce wuta ta kama ne lokacin mutane je ɗibar mai sakamakon faɗuwarta, abinda ya kai ga asarar rayuka.

Wani   shaidan gani da ido ya shaidawa jaridar Daily Trust cewar ya ga gawarwakin mutanen da suka mutu da suka kai 100, yayin da wasu da dama suka jikkata.

A watan octoban shekara 2024 da ta gabata akalla 140  suka mutu sakamamon konewar da suka yi lokacin da wata babar motar daukar mai ta kama da wuta a jihar Jigawa dake Najeriya.

Daruruwan mutane ne ke mutuwa  sakamakon hadurran tankokin mai a sassa daban-daban na Najeriya.

A wasu lokuta, akasarin wadanda abin ke rutsawa da su, mutane ne da ke taruwa a kusa da motar dakon man domin dibar mai daga cikin tankar kafin wani mummunan abu ya afku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)