Wasu majiyoyin jami’an jinya a asibitin koyarwa na birnin El- Fasher sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa a juma’ar makon jiya kaɗai hare-haren na dakarun RSF da suka riƙa kaiwa da makaman atilari sun hallaka mutane 30 tare da jikkata gommai, duk da kiraye-kirayen shugabannin ƙasashen duniya na kawo ƙarshen wahalar da al’ummar ƙasar ta Sudan suka faɗa sakamakon yaƙin na watanni 17.
Dakarun na RSF waɗanda su ke riƙe da ikon babban birnin na arewacin Darfur ko a Alhamis ɗin makon na jiya sai da hare-harensu kan wata kasuwa ya hallaka mutane 18 nan take, a wani yanayi da hatta jami’an lafiya ke rasa rayukansu a hannun mayaƙan waɗanda batun hare-harensu ya mamaye zaman babban zauren Majalisar ɗinkin duniya da aka ƙarƙare a ƙarshen mako.
Asibitin koyarwar birnin na Al-Fasher shi ne ɗaya tilo da ya rage a birnin ya ke iya karɓar marasa lafiya a kaf birnin, batun da jakadiyar Amurka a Majalisar ɗinkin duniya Linda Thomas-Greenfield ke cewa dole a tsagaita wuta ko don shigar da kayakin agaji musamman a Khartoum da El-Fasher da sauran sassan da ke tsananin buƙatar agaji.
A ɓangare guda sakatare janar na Majalisar Antonio Guterres ya roƙi ɓangarorin mayaƙan na RSF da Sojin Sudan kan su hau teburin sulhu don sassauta raɗaɗin da al’ummar ƙasar ke sha sanadiyyar yaƙin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI