An sanar da cewa sakamakon zabtarewar kasa a wani mahakar ma’adanai a Jamhoriyar Demokradiyyar Congo mutum uku sun rasa rayukansu inda kuma daya ya bata.
Lamarin ya faru ne a yankin Kasongo a Mukulungu mai nisan kilomita 11 daga garin Bikenge babban garin da ake hakar ma’adanai a yankin Maniema.
Wani jami’in gwamnatin yankin Claude Malisawa ya shaidawa manema labarai da cewa an gano gawarwaki uku da kuma mutum daya da aka garzaya dashi asibiti sanadiyar samu raunuka.