An sanar da cewa a harin bindiga da aka kai a wani kauye dake Ethiopia an kashe farar hula har 222.
A ranar Laraba ne dai wasu 'yan bindiga suka kai hari a wani kauye dake yammacin kasar lamarin da ya sanya fiye da mutum dubu 40 yin kaura daga matsugunansu.
Gwamnatin ta zargi kungiyar 'yan tawayen Tigray da laifin haifar da rikicin da ke ta'azzara a yankin a' yan watannin nan.
Dakarun Ethiopia sun bayyyana cewa sun magance mutum 42 daga cikin wadanda suka kai harin.
Firaiministan kasar Abiy Ahmed y bayyana harin a matsayin harin kisan kiyashi.