An sanar da cewa a wani rikicin kabilanci a jihar Edo dake kasar Najeriya mutum 18 sun rasa rayukansu.
Kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito hukumomin jihar Edo sun sanar da cewa a Benin babban birnin jihar rikici ya barke tsakanin wasu kabilu lamarin da yayi sanadiyar rayukan mutum 18 daga cikinsu har da 'yan sanda biyu.
Haka kuma a rikicin mutane da dama sun raunana, da yawan gidaje kuma an konesu kurmus.
Tuni dai jami'an tsaro sun kewaye yankin domin samar da lumana.