Mutane 16 ne suka rasa rayukansu a wani samame da aka kai kan motar daukar fasinja a jihar Kano a Najeriya.
Kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka sanar, wasu wadanda ba a san ko su wanenen ba suka kaiwa motar fasinjan da ta taso daga Abuja zuwa Kano hari kusa da yankin Danbatta.
A samamen da aka kaiwa motar a yankin Dambatta mutum 16 suka rasa rayukansu inda kuma wasu da dama suka raunana.
Gwamnan jihar Kano Abdullah Umar Ganduje ya yi tir da Allah wadai akan harin inda ya bayar da umarnin aikawa da jami'an tsaro a yankin da kuma fara bincike akan lamarin.