Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Rahotanni, sun bayyana cewa turmutsutsin ya faru ne lokacin da ake raba tallafin abinci a cocin.

Rundunar  yan sandan Abuja, ta tabbatar da aukuwar lamarin tare da adadin waɗanda suka mutu.

Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta ce yara huɗu na daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu.

Hakazalika, ta ce mutum takwas sun samu raunuka daban-daban.

“Mutum huɗu daga cikin waɗanda suka jikkata an sallame su bayan samun kulawa a asibiti,” in ji SP Adeh.

Bayanai, sun nuna cewa an shirya rabon tallafin ne don taimaka wa mabuƙata yayin shirin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Wasu da suka shaida faruwar lamarin, sun ce turmutsutsin ya faru ne da misalin karfe 7 na safiyar ranar Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)