Mutane sun mutu a yunkurin fasa gidan yarin a Congo

Mutane sun mutu a yunkurin fasa gidan yarin a Congo

Shedun gani da ido sun ce harin fasa gidan yarin da aka kai ya yi sanadiyar mutuwar gwamman mutane, duk da dai gwamnatin kasar ta ce mutane biyu kawai suka rasa ransu.

Kakakin gwamnatin kasar Patrick Muyaya wanda ke cikin tawagar shugaban kasar Felix Tshisekedi da ke China don halartar taro, ya ce manyan jami’an tsaron kasar sun isa wajen da abin ya faru don tabbatar da dai-daiton lamura.

Ministan shari’ar kasar Constant Mutamba, ya ce suna nan suna gudanar da bincike don hukunta wadanda ke da wannan wajen kitsa fasa gidan yarin.

Wannan dai ba shine karo na farko da ake kaiwa gidan yarin harin ba, domin ko a shekarar 2017 sai da aka fasa shi inda kusan fursunoni dubu 4 suka tsere.

Shi dai gidan yarin na Makala an gina shine da zummar daukar fursunoni dubu daya da dari 5, sai dai alkaluman hukumomin kasar na nuna cewa akwai kimanin fursunoni dubu 14 zuwa 15 da ake tsare da su a ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)