Ofishin Firaministan Uganda da jami’an ƴan sanda sun bayyana cewa iftila’in zaftarewar ƙasar ya faru ne a yankin Bulambuli a ranar Laraba, aƙalla kilomita 300 daga gabashin babban birnin ƙasar Kampala.
Ƙungiyar agaji ta Red Cross a Uganda ta ce aƙalla gidaje 40 ne laka ta binne su gaba ɗaya, yayin da wasu suka lalace.
Charles Odongtho, mai magana da yawun ofishin firaministan ƙasar mai lura da bala’o’i, ya ce mutane 15 ne suka rasa rayukansu yayin da ake fargabar da yawa na ƙarƙashin ƙasa.
Ya kara da cewa sama da mutane 100 ne ba’a gani ba a ƙauyuka 8 da lamarin ya faru, a gefe guda kuma an takaita zirga-zirga saboda yadda ruwan ya shafe tituna da hakan ya hana gudanar da ayyukan jin ƙai.
Uganda na fama da mamakon ruwan sama da ba’a saba gani ba tun daga watan Oktoban bana, lamarin da ke janyo ambaliyar ruwa da zaftewar ƙasa a wasu yankunan ƙasar.
Hukumar kula da tituna da rundunar ƴan sandan Uganda sun bayyana cewa, mamakon ruwan saman da aka yi ranar talata ya hadddasa tumbatsar kogin Nilu, da ya kai ga samun ambaliyar ruwa a ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI