Al’ummar ta Malawi sun samu kansu a wannan hali ne sakamakon mummunan fari da ya samo asali a sanadiyar ɗaukewar ruwan sama, bayan da guguwar El-nino ta yi matukar barna a ƙasar.
Mutanen sun ci gaba da kalace da doyar duk kuwa da fargabar da ake da ita kan irin mummunar illar da za ta iya yi wa lafiyar bil'adama.
Wata dattijuwa mai suna Manesi Levison mai shekaru 76 ta bayyana cewa sukan dafa doyar a kan wuta na tsawon sa’o’i 8 domin tabbatar da ganin gubar ta fita daga jikinta kafin su iya ci, inda ta bayyana cewa wani lokacin ƙananan yara kan shafe kwanaki uku kafin su samu abin da za su ci.
Sauyin yanayi na taka rawa wajen haddasa ƙarancin abinci AP - Tsvangirayi MukwazhiCin doyar kan haddasa mutuwa ko rashin lafiya, don haka dafa ta na tsawon lokaci ne ke cire gubar daga cikinta kafin su ci.
Dattijuwar ta ƙara da cewa ruwan sama ya tsaya a yankin ne tun a watan Afrilu, lamarin da ya haddasa konewar shuke-shuke a gonaki.
A yayin da dagacin kauyen mai mutum sama da dubu 1 da ke da tazarar kilomita 80 daga babban birnin ƙasar, ya bayyana cewa tun da aka fuskanci wannan iftila’i, sai a watan Maris ɗin shekara mai zuwa za su sake shiga gonakinsu domin aikin noma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI