Mutane miliyan 8.7 na bukatar taimakon jin kai a Najeriya

Mutane miliyan 8.7 na bukatar taimakon jin kai a Najeriya

An bayyana cewa mutane miliyan 8.7 na bukatar taimakon jin kai na gaggawa saboda hare -haren ta'addanci a arewa maso gabashin Najeriya.

A cewar rahotanni a kafafen yada labaran kasar Najeriya, mai kula da taimakon jin kai na Majalisar Dinkin Duniya Edward Kallon ya fada a wani Taron Majalisar Cigaban Kasa da aka gudanar a Maiduguri, cewa daya daga cikin manyan matsalolin jin kai a duniya an ci karo da su ne a arewa maso gabashin kasar.

Da yake lura cewa mutane miliyan 8.7 a yankin na bukatar taimakon gaggawa, Kallon ya ce sama da mutane miliyan 4.4 na bukatar agajin abinci cikin gaggawa.

Da yake bayanin cewa ana ci gaba da samun matsalolin kiwon lafiya sakamakon hare -haren kungiyar ta'adda ta Boko Haram, Kallon ya ce wadanda ke tsere wa hare -haren kungiyar na ci gaba da zama a sansanonin da keda cunkoson jama'a.

Kallon ya yaba da kokarin gwamnatin jihar akan magance yanayin, yana mai jaddada cewa kawai mafita ga rikicin shi ne zaman lafiya.

Fiye da mutane dubu 20 ne suka mutu a munanan ayyukan tashin hankalin da Boko Haram ta shirya, kungiyar da ta bulla a shekarar 2000 ta kuma fara ayyukan kin kari a shekarar 2009.

Daruruwan dubban mutane ne suka yi hijira saboda hare -haren ta'addanci da rikice -rikice a kasar ta Najeriya.


News Source:   ()