An bayyana cewa mutane kimanin miliyan 1,3 sun rasa matsugunansu a shekarar 2020 a Somaliya.
Ofishin Aiyukan Jin Kai na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da sanarwa a rubuce cewa, akwai mutane miliyan 2,9 da suka rasa matsugunansu a Somaliya, kuma miliyan 1,6 na bukatar taimakon gaggawa.
Sanarwar ta ja hankali da cewa, ana samun karuwar ibtila'o'i sakamakon ambaliyar ruwa, fari da sauyin yanayi a Somaliya, a shekarar 2020 ambaliyar ruwa ta illata mutane miliyan 2, yayinda guguwar Gati da ta kunna kai kasar a watan Nuwamban 2020 ta raba sama da mutane dubu 120 da matsugunansu.
A ranar 15 ga Fabrairun 2021, gwamnatin Somaliya da Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana ana bukatar dala biliyan daya domin taimakon jin kai a kasar.