Mutane miliyan 12 na fuskantar karancin cimaka a Afiirka ta Kudu

Mutane miliyan 12 na fuskantar karancin cimaka a Afiirka ta Kudu

A Afirka ta Kudu da ta kasance daya daga cikin manyan kasashen Afirka, mutane miliyan 12 na fama da matsalar karancin abinci.

Tarayyar Turai, Kungiyar Kare Fararen Hula da Sashen Aiyukan Tallafin Jin Kai sun fitar da rubutacciyar sanarwa inda aka bayyana cewa, annobar Corona, karancin abinci da rashin aikin yi sun janyo matsalar cimaka a Afirka ta Kudu.

Sanarwar ta ce "Kusan kaso 20 na al'umar kasar su miliyan 12 tun watn Satumban 2020 suke fama da matsalar karancin abinci."

Sanarwar ta ja hankali kan yiwuwar mumunanar halin da ake ciki a Afirka ta Kudu.

An bayyana cewa, mutane da dama sun rasa aiyukan yi, kuma farashin kayan abinci ya tashi da kaso 30.

An samu sama da mutane miliyan 1,5 dauke da cutar Corona a Afrka ta Kudu, kuma mutane sama da dubu 50 cutar ta yi ajali a kasar.

Afirka ta Kudu ce kasar da aka samu mafi yawan kamuwa da Corona a nahiyar Afirka.


News Source:   ()