Mutane dubu 950 na bukatar taimakon gaggawa a Mozambik

Mutane dubu 950 na bukatar taimakon gaggawa a Mozambik

Sakamakon hare-haren kungiyar ta'adda ta Ansarul Sunnah a Mozambik an bayyana cewa, mutane dubu 950 na bukatar taimakon jin kai na gaggawa.

Daraktan Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP) a Mozambik Antonella Daprille ya ziyarci Tsibirin Pemba da 'yan kasar Mozambik ke naman mafaka inda ya yi jawabi ga manema labarai.

Daprille ya ce, akwai mutane dubu 950 da ke bukatar taimakon jin kai na gaggawa a kasar.

Ya kara da cewa, "Mutane da dama sun gudu kuma wadanda suka rage ma a firgice suke."

Kusan mutane dubu 700 ne suka gujewa hare-haren Ansarul Sunnah a Mozambik.

Shekaru 4 da suka gabata kungiyar ta bulla a yankin Cabo Delgado mai arzikin man fetur da albarkarun kasa da ke iyaka da Tanzaniya inda ya zuwa yau ta kashe mutane sama da dubu 2.

Al'umar yankin na kira kungiyar da ke da alaka da 'yan ta'addar Daesh da suna Al-Shabab.


News Source:   ()