Sakamakon rikicin yankin Tigray na Itopiya, mutane dubu 78 ne suka yi gudun hijira zuwa kasar Sudan.
Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Sudan ta fitar ta bayyana cewa, Mataimakin Kwamishinan Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula da 'Yan Gudun Hijira a Sudan Raouf Mazo ya ziyarci sansanonin 'yan gudun hijira na jihohin Kasele da Gadarif da ke Sudan inda 'yan gudun hijirar Itopiya suke zaune.
'Yan gudun hijirar da ke sansanonin Umm Rakuba da Tandeba sun bayyanawa jami'in matsalolin kayan kula da lafiya, lantarki, ruwan sha da ilimin yaransu.
Rahoton da Ofishin Kwamishinan na Sudan ya fitar ya bayyana cewa, mutane dubu 78 ne suka yi gudun hijira daga yankin Tigray na Itopiya zuwa kasar.