Mutane dubu 30 na bukatar taimakon gaggawa a Mozambik

Mutane dubu 30 na bukatar taimakon gaggawa a Mozambik

Mutane kimanin dubu 30 ne ke bukatar taimakon jin kai sakamakon hare-haren da kungiyar ta'adda ta Ansarul Sunnah ta ke kai wa a kasar Mozambik da ke Kudancin Afirka.

Labaran da jaridun kasar suka fitar sun rawaito Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa da Magance Annoba ta Mozambik na cewa, kusan mutane dubu 9 daga cikin dubu 40 da ke zaune a yankin Palma ne suka yi gudun hijira zuwa yankunan Pemba, Mueda, Nangade da Montepuez.

Sanarwar ta ce, sakamakon hare-haren Palma, akwai mutane kimanin dubu 30 da ke bukatar taimakon jin kai.

A gefe guda, gwamnatin Mozambik ta bayyana za ta kai kayan taimako na dala miliyan 585 zuwa yankin a cikin wata daya mai zuwa.

Sama da mutane dubu 670 ne suka yi gudun hijira a kasar Mozambik sakamakon hare-haren kungiyar ta'adda ta Ansrul SUnnah.

Shekaru 4 da suka gabata kungiyar Ansarul Sunnah ta bulla a yankin Cabo Delgado da ke da arzikin iskar gas da man fetur a iyakar Mozambik da Tanzaniya. Ya zuwa yau mutane sama da dubu 2 sun mutu sakamakon hare-haren kungiyar.

Ana zargin kungiyar na da alaka da 'yan ta'addar Daesh, al'umar yankin na kiran ta da sunan Al-Shabab.


News Source:   ()