Adadin wadanda sutar kwalara ta yi ajali a Najeriya ya karu zuwa mutane dubu 1,768.
Hukumar Yaki da Cututtuka ta Najeriya NCDC ta fitar da rahotonta na mako-mako inda a mako dayan da ya gabata cutar takashe karin mutane 72.
Tun daga watan Janairu cutar kwalara na ci gaba da yaduwa a jihohin Najeriya da Abuja Babban Birnin Kasar.
A wannan lokaci, cutar ta kama mutane dubu 47,603 inda adadin wadanda ta kashe kuma ya kama dubu 1,768.
Shanruwa ko abinci da ke dauke da kwayoyin cuta na "VibrioCholerae" ne ke janyo kamuwa da cutar. Tana janyo amai da gudawa da rasa ruwan jiki wanda idan ba a dauki matakin magani da wuri ta ke yin ajalin wadanda suka kamu.