Wani likita daga asibitin yankin na N’Zerekore da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, akwai gawarwaki kimanin 100 kwance a asibitin, waɗanda suka rasa rayukansu sanadiyar rikicin.
Wani faifan bidiyon da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuna gawarwaki yashe a kan titi kusa da filin wasan da rikicin ya tashi.
Wani ganau ya ce rikicin ya tashi ne sakamakon wani mataki da alkalin wasa ya ɗauka, lamarin ya sanya magoya bayan daya daga cikin ƙungiyoyin da ke wasan kutsa kai cikin fili.
A cewar wata kafar yaɗa labaran ƙasar, an shirya wasan ne da nufin karrama shugaban gwamnatin sojin ƙasar Mamadi Doumbouya, wanda ya kwace mulki a shekarar 2021.
Shirya irin waɗan nan wasanni a yankin Yammacin Afrika dai ba sabon abu bane, musamman ga masu rike da muƙaman gwamnati da ƴan kasuwa da dai sauransu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI