Mutane 33 sun rasa rayukansu sakamakon kifewar wani jirgin ruwan kwale-kale a kogin Albert a kan hanyar zuwa Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo daga Uganda.
Jami'in yankin Wangongo da ke jihar Ituri ta Jamhuriyar Kongo Vital Adubanga ya shaida cewar, jirgin ya kife da kusa da kauyen Kolokoto, kuma mafi yawan wadanda suka mutu 'yan kasar Kongo ne da dokar hana zirga-zirga saboda Corona ta hana dawowa kasashensu ta hanyoyin mota.
Ya ce "Ya zuwa yanzu mutane 33 sun mutu, an kuma gano wasu 7 da ransu."
Adubanga ya kara da cewar, sakamakon dokar hana fita, 'yan kasuwar Kongo da dama sun makale a Uganda, kuma suna hawa jiragen ruwa da daddare a Kogin Albert tare da kama hanyar dawowa kasarsu.
Ana tunanin tsananin iska ne ya janyo hatsarin.